Romans 8

Rai Ta Wurin Ruhu

1Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, 2gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ʼyantar da ni daga Dokar Musa. 3Gama abin da dokar ba ta iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi saʼad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yǎ zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi. 4Ya yi haka domin yǎ cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.

5Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan shaʼawace-shawaʼacen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so. 6Ƙwallafa rai ga alʼamuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga alʼamuran Ruhu kuwa rai ne da salama; 7hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba. 8Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.

9Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne. 10Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci. 11In kuwa Ruhu wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya ta da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.

12Saboda haka ʼyanʼuwa, muna da hakki-amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba. 13Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu, 14domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ʼyaʼyan Allah. 15Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “Abba,
Aramayik na Uba
Uba.”
16Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ʼyaʼyan Allah ne. 17In kuwa mu ʼyaʼya ne, to, mu magāda ne-magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.

Ɗaukaka Ta Nan Gaba

18A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. 19Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ʼyaʼyan Allah. 20Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21cewa za a ʼyantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ʼyancin ɗaukakar ʼyaʼyan Allah.

22Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yǎ zuwa wannan lokaci. 23Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ʼyaʼyan riƙo na Allah, fansar jikunanmu. 24Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu? 25Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.

26Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin adduʼa ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa. 27Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.

Fiye da Masu Nasara

28Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa,
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da, A cikin dukan alʼamura Allah
yana
Ko kuwa aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa; waɗansu rubuce-rubucen hannu kuma suna da, dukan alʼamura suna aikata tare zuwa ga alheri ga masu ƙaunar Allah
waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
29Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yǎ zama ɗan fari cikin ʼyanʼuwa masu yawa. 30Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.

31Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka-ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba? 33Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa. 34Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu-fiye da haka ma, shi da aka ta da zuwa rai-yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu. 35Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36Kamar yadda yake a rubuce cewa:

“Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;
an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”
Zab 44.22

37Aʼa, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko malaʼiku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Copyright information for HauSRK